6 Faburairu 2016 - 14:57
CIGABA A MILLOLI DA AQEEDU NA SHEIKH HAMZA LAWAL

FA’IDA TA HUDU NA DARASIN AL-MILAL WAN NIHAL HALASCIN TSINEWA YAZID DA KAFIRTA SHI A WAJEN WASU MALAMAN SUNNAH MARTANIN UMMUL MU’UMININA A’ISHAH GA MARWAN DAN HAKAM

  A baya mun fadi wata ka’ida ta su Ibn Taimiyyah wadda suke cewa: “Barin sunnah ita tafi idan ya kasance ‘yan shi’a sun yi riko da ita (wannan sunnan) gamgam”.Daga nan ne muka shiga cikin littafin Ruhul Bayan wanda yayi bayanin irin abin da ya kamata mutum yayi a ranar Ashura.Yace ka da mutum yayi farin cikin kamar yanda Yazid la’ananne yake yi sannan ka da yayi bakin ciki kamar yanda Rafida da Kawarij suke yi.A wannan wurin ne muka shiga babin halascin tsine ma Yazid a wajen malaman Sunnah da kuma halascin kafirta Yazid a wajen wasu malaman Sunnah din. Muke cewa wadannan bahsosin idan mutum ya lura zai ga wa’yanda suka cika duniya da kururuwa na zagi da cin mutumci da karyace karyace akan shi’a,suna yi ne saboda ka da gaskiya ta fita.Amma ita gaskiya sai ta fita kamar yanda Allah (T) Yake cewa:FAWAQA’AL HAQQU WA BADALA MA KANU YA’AMALUN”.Me suka cewa Musa(as) a suratul A’araf?kai zaka jefa ko NAHNUL MULQUM  ma’ana ko mu zamu jefa FA LAMMA ALQU SAHARU A’AYUNAN NAS WASTARHABUHUM WA JA’U BI SIHRIN AZIM,FA AUHAINA ILA MUSA AN ANQI ASAH,su suka fara jefa sandunan su (wato Saharata Fir’auna nake nufi)to sai muka(Allah) yiwa Musa wahayi muka shiryatar dashi akan ya jefa sandan sa sai ya jefa sai ta zama gumurcin maciji ,sai Allah yace FAWAQA’AL HAQQU WA BADALA MA KANU YA’AMALUN,FA GULIBU HUNALIKA WANKALABU SAGIRIN. Su sukan yi jidali da BADIL wato jidali da karya domin su danne gaskiya.Saboda akwai isharori masu yawan gaske akan cewa duk yanda aka yi a rufe gaskiya ba zata rufu ba.Saboda haka sharrace sharrace da kage kage da zuwa da hadisai wadanda ba a san daman su balle hagun su.Bid dabi’atul hal da mutum ma’abucin karatu ne da dalibta zai sani akan cewa ba a hukunta mutane da littafan hadisan su,amma saboda mutum shi ba ahalin fanni bane ya shiga cikin shi sai yama kowanne abu zai tawahhumi daga gare shi wato komai zai iya yi tun da yana tafiya ne ba akan asasin  linzami da ka’idoji ba. Ala kulli hal,kaman yanda suka ce “WAMA ISHTA AYATAD DAHRI AJABA”ma’ana:matukar zaka rayu to zamani zai nuna maka abubuwa masu ban mamaki.Ba’un su zata yi ja amma ba zasu bar ba’un din ka ta ja ba,wato kenan awo da ma’aunai guda biyu. Mun zo in da Ummul Mu’uminina Aishah take shedawa cewa Manzon Allah(sawa) ya tsine ma Marwan a lokacin yana tsatson mahaifin shi.Wannan akwai shi a cikin Durrul Mansur na Allamah Jalalud Din Suyudi a wurin WAMA JA’ALNAL RU’UYAL LATIY ARAINAKA ILLA FITNATAN LIN NASIY WASH SHAJARATAL MAL’UNATA FIL QUR’AN,mutum ya duba wannan wurin. Sannan Ibn Abi Hatim ya rawaito daga Abdullahi Ibn Umar cewa Annabi(sawa) Yace: “Na ga ‘ya’yan Al-Hakam dan Abil As-wato mahaifin Marwan-akan mimbari na kamar kai kace su birai ne”. Dab’an,ba zan boye maku asiri ba akan cewa in kun tuna da hadisin da muka karanta daga Imamul Bukhari inda Manzon Allah (sawa) yake cewa “Halakar al’umma ta-hadisin Abu Huraira- zata faru ne akan hannayen kanana-kananan  yara wawaye.A lokacin Abu Huraira na cewa da na so da na fada maku cewa ‘ya’yan FULAN da FULAN ne,kun san bai fadi su waye fulan da fulan din ba.To zan fada maku su waye FULAN da FULAN din. A cikin Hudas Sariy Muqaddima din Fathul Bariy sharhin Sahihul Bukhari.Shi Ibn Hajril Asqalani din yana cewa “KITABUL FITNATI NA’UZU BILLAHI MIN HA”ma’ana:littafin Alfitna muna neman tsarin Allah mai girma daga ita.Sai yace: “HADITHU ABI HURAIRAH RADIYALLAHU ANHU,LAU SHI’ITU AN AQULU BANIL FULAN WA BANIL FULAN”ma’ana :da na so nace ‘ya’yan wane ne da ‘ya’yan wane ne da nace-Ibn Hajar ke fadin wannan-Sai yace  Abu Hurairah na nufin ‘ya’yan Banu Marwan ne da ‘ya’yan Mu’awiyah. Akwai shi a cikin Mustadraku Alas Sahihaini na Al-Hakim,ya rawaito shi yana cewa “WA HAZAH HADISUN SAHIHUL ISNAD”daga Ummul Mu’uminina Aishah daga AbdurRahman bn Auf.Sannan ban da wannan akwai wani hadisi mai muhimminci wanda Hakim din ya rawaito a Mustadrak din AN MUHAMMAD BIN ZIYAD yana cewa “LAMMA BAYA’A MU’AWIYA LIBNIHI YAZID”lokacin da Mu’awiya dan Abi Sufyan yayi mubaya’a ga dan shi Yazid-kun san yana da rai ya sanya shi WALIYUL AHAD wato magaji ko yarima ban sani ba,ko ciroma a wasu garuruwa idan aka cewa mutum ciroma wato shi zai zama sarki,ko magajin gari-lokacin Mu’awiya ya shawarci dukkan Sahabbai gabaki daya akan nada shi wannan matsayin amma babu ko daya wanda ya yarda daga cikin Sahabbai-masu cewa Yazid  radiyallahu anhu su ji wannan sosa- dukkan sahabbai basu yarda ba sun ma yi inkarin wannan kuduri ko mataki na Mua’awiya,to sai Marwan yace jiya a barci Allah ya nuna min cewa ya nada shi-yanzu wannan aikin Allah ne,daga nan ne Al-Jabru ya samo asali da kuma kaddara da sauransu.Kila wata rana zamu yi magana akan wannan,cewa Kaddara kowa dole yayi imani da ita,saidai Kaddara da Jabru cewa komai Allah ne yayi wannan daga lokacin ya faro.Hakim yana cewa lokacin da Mu’awiya ya amshi bai’a ma Yazid “KALA MARWAN IBN HAKAM SUNNATU ABI BAKAR WA UMAR”sai Marwan dan Hakam yace kayi daidai wannan itace sunnan Abubakar da Umar-sai ya yiwa Abubakar da Umar kage.Wannan ya nuna maka akwai sunnoni masu yawa-Wato Marwan yana tabbatar da abin da Mu’awiya yayi na daukan bai’a ga Yazid.To a lokacin akwai AbdurRahman Ibn Abubakar a wajen sai yace ba sunnar Abubakar da Umar bace saidai sunnar sarkin Rum da Farisa saboda su suke sa aka gaje su.A wannan lokacin sai Marwan ya ji haushin AbdurRahma bin Abubakar saboda inkarin da’awan sa da  yayi akan cewa matakin da Mu’awiya ya dauka yayi daidai da sunnan Abubakar da Umar.Nan da nan sai Marwan ya zagi AbdurRahman Ibn Abubakar yace ba kai ne wanda Allah ya saukar dangane da kai “WALLAZI QALA LI WALIDAIHI UFFIN LAKUMA ATA’IDANINIY….”wannan wanda yace ma iyayensa tir daku-da na gari yana zargin dan da ba nagari ba-Sai mai riwaya yake cewa a lokacin da labari ya kai wa Aishah dangane da jayayyan Marwan da AbdurRahman,sai tace Marwan yayi karya wallahi,MA HUWA BIHA wato ba akan shit a sauka ba WALAKINNA RASULULLAH(SAWA) LA’ANA ABA MARWAN WA MARWAN FI SULBIHI wato amma Manzon Allah (sawa)ya la’anci mahaifin Marwan alhalin Marwan yana cikin tsatsonshi-Aishah tana raddi ga Marwan akan martanin da yayi wa dan uwan ta AbdurRahman-FA MARWAN BA’ADA MAN LA’ANAHULLAH ma’ana Marwan sashi ne na wadanda Allah ya tsine ma.Sai Hakim yace HAZA HADISUN SAHIHUL ISNAD ALA SHARDISH SHAIKHAIN ma’ana wannan hadisi ne mai ingancin isnadi a sharadin shehunai guda biyu.288